1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taɓa ka Lashe: 14.10.2009

October 14, 2009

A bana wata ´yar Romaniya amma ´yar asalin Jamus Herta Müller ta ci kyautar Nobel da ake bawa marubuta adabi.

https://p.dw.com/p/K5vl

Ita dai Hetta Müller ta tashi ne a ƙasar Romaniya a cikin wani yanayin rayuwa da ta kwatanta da makaranta ta tsoro musamman a cikin rubuce rubucenta. Tun a cikin shekarun 1990 an fassara littattafanta a cikin harsuna fiye da 20 kuma ta kasance ɗaya daga cikin mashahuran marubuta adabi a duniya. Wannan marubuciyar adabi mai shekaru 56 da haihuwa a shekarar 1987 da ita da mijinta suka shigo nan Jamus.