1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a kan tsarin yin zaɓe a Najeriya

Uwais Abubakar IdrisMarch 5, 2015

Wasu ‘yan majalisun na nuna rashin amincewarsu da sabon tsarin amafani da akwatina uku wajen zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun.

https://p.dw.com/p/1EmNW
Nigeria Wahlkommision verschiebt Wahltermin Attahiru Jega
Shugaban hukumar zaben Najeriya Attahiru JegaHoto: Stringer/AFP/Getty Images

Hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana cewar tana da isassun kuɗaɗen da za ta gudanar da ɗaukacin zaɓuɓɓukan da za ta gudanar a dai dai lokacin da wasu ‘yan majalisun ke nuna rashin amincewarsu da sabon tsarin amafani da akwatina uku wajen zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun.

Tsarin wani sabon salo ne wanda hukumar ta soma aiki da shi a karon farko

To wannan tsarin na amafani da akwatina uku don jefa ƙuri'a ga shugaban ƙasa da sanata da kuma 'yan majalisar wakilan wanda a karon farko hukumar zabe ta ɓullo da shi na zaman sabon salo. Abin da ya ɗaga hankali a kan batun shi ne zayyana cewar duk ƙuri'ar da bisa kuskure ta faɗa akwatin da bai dace a sanyata ba to za ta kasance ɓataciyya. Ko da kuwa mai zaɓen ya dangwalla hannu a dai dai wurin da ya dace, wanda a can baya ba haka tsarin yake ba. Sanata Kabiru Gaya ɗan majalisar dattawan Najeriya ne ya ce akwai dalilin da ya sanya suke da ja da wannan sabon tsari.

Wahlen Nigeria Ergebnis
Shugaban hukumar zaben Najeriya Attahiru Jega tare da wasu sauran jama'AHoto: AP

‘'A ƙaida kana da dama ka yi zaɓe, amma bayan ka yi zaɓen don kawai ka yi kuskure ka jefa ƙuri'ar a wani akwati sai a ce baka yi dai dai ba, saboda haka wannan zai kawo rikici a zaɓen gaba ɗayansa.''

Hukumar ta dage cewar sauƙi ne ta kawo ga al'amuran zaɓen

Ita dai hukumar zaɓen Najeriyar na mai dagewa da cewar ta fito da tsarin ne da nufin sauƙaƙa gudanar da zaɓuɓɓukan da a baya a kan kwashe lokaci mai tsawo wajen rarrabe ƙuri'un. Wasu 'yan siyasar dai na gani cewar a kwai lauje cikin naɗi abin da hukumar ta ce ba haka ba ne Mr Nick Dazzan shi ne mataimakin daraktan hulda da jama'a na hukumar zaɓen Najeriyar.

Wahlen Nigeria Ergebnis
Shugaban hukumar zaben Najeriya Attahiru Jega da farar rigaHoto: dapd

'' Kafin a fara ƙidayar ƙuri'un sai an tantance duk ƙuru'un da aka kaɗa a kowane akwati. Kafin ka fara jefa ƙuri'a ma yakamayta ka yi la'akari da cewar akwatina uku ne domin zaɓen na mutane uku ne ke takara daban- daban. Ko da yake lokaci ya ƙure amma za mu ƙara wayar da kan jama'a a kan wannan batu.''

A yayin da wannan sabuwar taƙaddam,a ta sake kuno kai a game da tsarin amafani da akwatinan jefa ƙuri'ar guda uku, da alamu da sauran aiki a gaba wajen wayar da kan jama'a musamman mazauna karakara a kan wannan tsari.