1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙƙaddama game da saban kundin tsarin mulki a Masar

November 27, 2012

'Yan adawar Masar sun zargi 'yan uwa musulmi da yunƙurin ƙaddamar da shari'a a kudin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/16qdQ
25/06/12 11:42:24 1929x2800(446kb) Muslim Brotherhood's president-elect Mohamed Morsy speaks during his first televised address to the nation in Cairo Muslim Brotherhood's president-elect Mohamed Morsy speaks during his first televised address to the nation at the Egyptian Television headquarters in Cairo June 24, 2012. Morsy's victory in Egypt's presidential election takes the Muslim Brotherhood's long power struggle with the military into a new round that will be fought inside the institutions of state themselves and may force new compromises on the Islamists. Picture taken June 24, 2012. To match Analysis EGYPT-ELECTION/STRUGGLE/ REUTERS/Stringer (EGYPT - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Mohammed MursiHoto: Reuters

A makon da ya gabata shugaban ƙasar Masar Mohamad Mursi ya ƙaddamar da wata doka mai ƙara masa ƙarfin mulki.

Wannan doka ta jefa Masar cikin sabuwar dambarwar siyasa ta fannin shirya zanga-zangogi tsakanin masu goyan baya da masu adawa da matakin na shugaba Mursi.

A baya-bayan nan, idan banda wakilan jam'iyar 'yan uwa musulmi da 'yan salafiya, kusan duk wakilan sauran jam'iyun siyasar ƙasar,sun yi murabus daga majalisar da aka ɗorawa yaunin rubuta kudin tsarin mulkin ƙasar.Hatta wakilan mujami'un ƙasar sun janye daga wannan majalisa,suna zargin 'yan uwa musulmi da ƙoƙarin saka shari'a addinin musulunci a cikin kundin tsarin mulkin.

A tunanin Mohammad Zaraa shugaban wata cibiyar kare haƙƙoƙin bani Adama da ke birnin Alkahira idan aka rubuta kundin tsarin mulkin ba tare da wakilan jama'a ba daga sassa daban-daban zai kawo nakasu ga wannan kundi:

Members of the ultra-conservative Salafist al-Nur party attend the first session of the Egyptian parliament since a popular uprising ousted Hosni Mubarak in Cairo on 23 January 2012.Egypt's first free parliamentary elections, which were held in phases between November and early January, saw Islamists clinch nearly three-quarters of the seats. AFP PHOTO/Asmaa WAGUIH/Pool (Photo credit should read ASMAA WAGUIH/AFP/Getty Images)
'Wakilan 'yan salafiyya a Majalisar MasarHoto: ASMAA WAGUIH/AFP/Getty Images

"Janyewar wasu wakilan daga majalisar rubuta kundin tsarin mulkin zai rage tasirin kundin.Majiyoyi sun tabbatar da cewa har yanzu gungun 'yan uwa musulmi na cigaba da rubuta kundin.

Kamata tayi a ce an samu haɗin kai wajen wannan aiki, ba wai kaɗai daga 'yan majalisar ba, har ma da daga al'umar ƙasa."

Mohamad Zaraa yace har ma an ɓullo da wani kundin tsarin mulki ta baya fage ranar 22 ga watan Oktoba da ya shuɗe,wanda sauran wakilan su ka ce ba su da masaniya kansa.

A cikin wannan yanayi ne shugaba Mohamad Mursi ya sauke babban antoni janar na ƙasa sannan kuma ya ƙarawa kansa ƙarfin mulki, matakin da masu adawa da shi su ka fassara da wani yunƙurin na wanzar da mulkin kama karya.

A halin da ake ciki abin na da kamar wuya sauran wakilan da ba na jam'iyar 'yan uwa musulmi ba,su koma aiki a cikin wannan majalisa.

Babban saɓani tsakanin su shine matsayin shari'ar addinin musulunci a cikin kudin tsarin mulki.

A tunanin jam'iyar 'yan uwa musulmi, cilas ne shari'a ta kasance madogara ga wannan saban kudi, matakin da sauran wakilai suka yi watsi da shi.

Protesters gather at Tahrir square in Cairo November 23, 2012. Angry youths hurled rocks at security forces and burned a police truck as thousands gathered in central Cairo to protest at Egyptian President Mohamed Mursi's decision to grab sweeping new powers. Police fired tear gas near Tahrir Square, heart of the 2011 uprising that toppled Hosni Mubarak at the height of the Arab Spring. Thousands demanded that Mursi should quit and accused him of launching a "coup". REUTERS/Mohamed Abd El Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Zanga-zanga a dandalin TahrirHoto: Reuters

Shima Mohammad Zaraa ya baiyana adawa da aniyar ƙaddamar da shari'ar musulunci a Masar ya kuma bada hujjojinsa:

"Ya ce bai dace ba a yi dogara da Alƙur'ani da aka rubuta shekaru fiye da dubu da suka wuce a matsayin dokoki a wannan zamani.

Aikata hakan zai rikiɗa Masar daga ƙasar inda kowa ke da 'yancin biyar addininsa zuwa ƙasar tsatsauran ra'ayin kishin Islama."

Wani daga ƙudurorin da ke tada hankalin masu adawa da shari'a a Masar shine girka wata rundunar mai kama da hukuma Hizba wadda za ta yaƙi da gurɓacewar tarbiyya da kuma tabbatar da bin tafarkin addinin Islama.Akwai irin wannan runduna a Saudi Arabiya.

Walid Abdel Majid wani ɗan ƙasar Masar mai adawa da ƙaddamar da shari'a a Masar yayi tsokaci akai:

"Wannan matakin da suke shirin sakawa a cikin kundin tsarin mulki zai haddasa fintintunu masu yawa, idan ba a yi takatsantan ba, wurin gyara za a tafka ɓarna".

Sakamakon dambarwar da ta sake ɓarkewa a fagen siyasar Masar,da alamun har yanzu tsugunne ba ta ƙare ba an saida kare an sayi biri.

Mawalladfi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani