1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara na fuskantar barazana a Siriya

Ahmed Salisu MNA
August 10, 2018

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce yara kimanin miliyan guda na cikin hadari a sansanonin 'yan gudun hijira a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/32zYe
Vom Krieg zerstörte Schulen in Syrien al-Saflaniyeh
Hoto: Reuters/K. Ashawi

Asusun UNICEF ya ce karancin ruwa da na magunguna da ake fuskanta a wannan yanki babbar barazana ce ga yara kazalika gwabza fadan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye shi ma na barazana ga rayuwar yaran. Gargadin na UNICEF na zuwa ne daidai lokacin da dakarun gwamnati suka yi barin wuta a wasu kauyuka da garuruwa, inda lamarin ya rutsa da wasu fararen hula ciki kuwa har da wani karamin yaro.