Syria ta yi alkawarin ba da cikakken hadin kai a binciken kisan Rafik Hariri | Labarai | DW | 01.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Syria ta yi alkawarin ba da cikakken hadin kai a binciken kisan Rafik Hariri

Syria ta yi alkawarin ba da hadin kai a binciken da MDD ke yi na kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri, bayan wani kudurin kwamitin sulhu da ya bukaci gwamnatin Damaskus da ta taimaka ko kuma a dauki matakai kanta. To sai dai duk da haka jami´ai da dubban ´yan Syria da suka bijirewa kudurin sun gudanar da zanga-zanga inda suka sake nanata cewar ba hannun Syria a kisan na Hariri, duk da cewa wani rahoton MDD ya shafawa manyan jami´an leken asirin kasar kashin kaji. Dukkan membobi 15 na kwamitin sulhu suka amince da kuduri wanda yayi kira ga Syria da ta tsare tare da hana dukkan mutanen ake zargi da hannu a kisan barin kasar kana kuma ta dora hanun kan kadarorinsu. A lokacin da yake mayar da martani kan kuduri cikin fushi ministan harkokin wajen Syria Faruq al-Shara ya zargi kwamitin sulhu da dorawa kasarsa laifin kisan Hariri bisa zato. Syria ta ce ba´a yi adalci ba a kudurin musamman saboda amincewa da shi ga baki daya da membobin kwamitin sulhun suka yi.