Switzerland: Layin dogon karkashin kasa mafi tsawo a duniya | Labarai | DW | 01.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Switzerland: Layin dogon karkashin kasa mafi tsawo a duniya

Kasar Switzerland ta bude layin dogo na karkashin kasa mafi tsawo a duniya da zai kawo sauki ga sufurin jiragen kasa.

Shugaban kasar Switzerland Johann Schneider-Ammann ya bude sabon layin dogo na karkashin kasa a kasar da ke kira Gotthard-Tunnel. Jiragen biyu dauke da mutane 500 suka tashi daga arewa da kuma kudu na layin dogon mai nesa kilomita 57 da kuma ke zama irinsa mafi tsawo a duniya. Shugaban ya yaba da bude hanyar da wata rana ta tarihi. An dauki tsawon shekaru 17 ana aikin layin dogon da ya ratsa karkashin tsunukan Alps. Aikin ya ci kudi Euro miliyan dubu 11. Hanyar za ta rage lokacin tafiya tsakanin biranin Zürich a Switzrland da Milan a Italiya da kwatankwacin awa daya, za ta kuma saukaka sufurin jirgin kasa tsakanin kasashe da ke kusa.