1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suu Kyi ta yi jawabin farko bayan sakinta.

November 14, 2010

'Yar fafutukar aiwatar da dimukuraɗiya a Burma , Aung San Suu Kyi ta yi jawabi ga magoya bayanta

https://p.dw.com/p/Q8Mb
Aung San Suu Kyi yayin da take jawabi ga magoya bayanta.Hoto: AP

A cikin jawabinta da ke zamata irinsa na farko cikin shekaru bakwai, shugabar jam'iyyar adawa a ƙasar Burma Aung San Suu Kyi ta ce ba ta yi fushi da gwamnatin sojan ƙasar bisa tsare ta da ta yi ba. Ta faɗa wa dubban magoya bayanta cewa tana buƙatar yin aiki tare da dukan ɓangarorin da ke gwagwarmayar wanzar da dimukuraɗiya, domin inganta rayuwar al'umar ƙasar. Shugabannin ƙasahen duniya sun bayyanar da jin daɗinsu game da sakin Suu Kyi bayan shekaru 15 da aka shafe ana tsare da ita. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce dagewa da gwagwarmayar da Suu Kyi ta yi a cikin limana, ya sanya ta a matsayin abar koyi a duniya. Kakakin babban sakataren Majlisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki- Moon ya kira Suu Kyi tamkar ƙwarin-gwiwa ga duniya baki ɗaya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu