1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An yi wa Aung San Suu Kyi daurin shekaru biyar a gidan yari

April 27, 2022

Bayan samun ta da laifin cin hanci, kotu a kasar Myanmar ta yanke wa hambararriyar shugabar kasar Aung San Suu Kyi daurin shekaru biyar na zaman kaso.

https://p.dw.com/p/4AVwn
Aung San Suu Kyi
Tsohuwar shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu KyiHoto: Dan Kitwood/PA Wire/empics/picture alliance

A asirce kotun da ke a Myanmar din ta yi zamanta har ta yanke wa tsohuwar shugabar kasar Aung San Suu Kyi hukuncin zaman kason na shekaru biyar. Kotun ta ce ta same ta da laifukan cin hanci. Wani tsohon minista da suka yi aiki tare da ita ne dai ya bayyana a gaban kotu ya bayar da tabbacin cewa shi da kansa ya ba Suu Kyi kyautar wani zinare a lokacin tana kan madafun iko.

Kazalika akwai zargin karbar rashawa da ta kai zunzurutun kudi Euro 560,000 da kotun ta Myanmar ta ce Suu Kyi din ta karba a shekarun baya. To sai dai wata 'yar fafutuka 'yar asalin Myanmarda yanzu haka ke a wajen kasar Wai Hnin Pwint Thon, ta ce babu kanshin gaskiya a zarge-zargen da ake yi wa Suu Kyi.

"Wadannan zarge-zarge ne marasa tushe ballantana makama. Bita da kullin siyasa ne kawai don ci gaba da tsare Suu Kyi a gidan kaso na dogon lokaci. Ya kamata sojojin su sani cewa matakin ba zai dakile tauraruwarta ba, maimakon haka ma mutane na ci gaba da yi wa sojojin turjiya har yau har magajin gobe.''

Karin Bayani: Shekara guda cikin halin kunci a Myanmar

Tun daga lokacin da sojoji dai suka hambarar da Suu kyi a farkon shekarar da ta gabata, jama'ar kasar ta daina ganin tsohuwar shugabar. Har yanzu babu wanda ya san inda ake tsare da ita. Haka kuma tun da aka fara gabatar da ita a gaban kotu sau daya ne hotan Suu Kyi din ya fito bainar jama'a. Shari'ar boye da hana jami'an ketare ganawa da Suu Kyi da sojoji masu mulkin Myanmar suka yi, na haifar da tsoro da shakku a kan hakikanin halin da take ciki.

Myanmar Naypyitaw | Militärparade am Armed Forces Day
Janar Min Aung Hlaing, shugaban mulkin sojaHoto: Aung Shine Oo/AP Photo/picture alliance

Rashin bayyanar Aung San Suu Kyi mai shekaru 76 dai a shari'o'i dabam-daban da ake yi mata a Myanmar ya sanya jama'a nuna fargaba kan lafiyarta a kokarin da take yi na gamsar da kotunan kasar cewa sharri da kage ne kawai ake mata. 

Wai Hnin Pwint Thon wace ita ma yanzu haka mahaifinta ke a gidan kaso a Myanmar bayan kama shi a wurin zanga-zanga, ta ce "Maimakon durkusar da 'yan adawa, hukuncin wannan Laraba da kotun Myanmar ta yanke wa Suu Kyi kan zargin cin hanci, zai kara wa 'yan adawa farin jini ne domin kowa ya san bita-da kullin siyasa ne." 

Karin Bayani: Kotu ta tsawaita daure Aung San Suu Kyi

Zarge-zargen da gwamnatin mulkin sojin Myanmar din dai ke yi wa Suu Kyi za su iya sanya ta zaman gidan kaso har sama da shekaru 150 masu zuwa, idan har aka tabbatar da su. Sai dai kuma masana na ganin sojojin sun yi haka ne domin dauke wa masu Zanga-zanga a kasar hankali daidai lokacin da suke kokarin tsara yadda za su fatattaki masu adawa da su. Kuma wasu ma na cewa koda Suu Kyi ta gabatar da hujjoji na yankan shakku da ke musanta zarge-zargen, da wuya sojojin su iya sakin ta kafin zaben shekara mai zuwa da sojojin kasar suka tsara gudanarwa