Sunjata Keita, Zakin Mandingue | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 15.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Sunjata Keita, Zakin Mandingue

Da sake hada Daular Afirka ta Yamma wacce ta kasance a rarrabe a karni na 13, Soundiata Keita ya kafa daular da har yau ta yi suna. Soundiata Keita ya kasance jarimi kana jagoran al'umma.

Rayuwarsa:

An haifi Sunjata ko kuma Soundiata Keita a Niani wani lardi a Daular Mandingue. Bayan mutuwar mahaifinsa sarki Nare Magham Konate ya yi hijira. Ya bayyana kansa a yaki da sarkin Sosso Soumaoro Kante kana ya zama Mansa sarkin sarakuna ke nan bayan da ya ci yakin Kirina a shekara ta 1235. Sannan ya mutu a shekara ta 1255, ya bar babbar daula.

 

An san shi:

Tarihin Soundiata Keita an rika yada shi a duniya daga gargajiya har ya zuwa na zamani, sai dai kuma ba dukkannin tarinhinsa ba ne aka rubuta.

Tarihin ya nuna cewar an haife shi gurgu. Wata rana Soundiata ya ga an ci mutuncin mahaifiyarsa, abin da ya sa ya fara tafiya da kafafunsa ke nan domin daukar mata fansa. Tafiyarsa ta farko ta kasance ta mazaje kamar yadda wani mai ba da labarinsa da tarihinsa da ake kira Mamadou Kouyate ya bayyana, wanda kuma malamin tarihi Djibril Tamsir Niane ya rubuta a cikin littafin da ya wallafa a 1960 (éditions Présence Africaine). Wato rukunin littattafai na Afirka.

A dubi bidiyo 01:55

Sunjata Keita na tsohuwar daukar Mali

Maharbi mai dadin hannu Soundiata ya hada daula a yammancin Afirka wacce ta kasance a rarrabe tun bayan faduwar Daular Ghana. Babbar nasararsa a yaki ita ce ta Kirina a 1235 da sarkin Sosso wacce a kanta ya zama sarkin sarakuna wato Mansa.

A karkashin daular, Soundiata ya shahara wajen hada kawunan kabilu tare da tsara al'umma da bai wa kowa kasar noma da kuma hakokin da suka dace, har ma ana yi masa lakabi da sunan tushen kare hakkin dan Adam. 

 

Rudani:

Saboda rashin tarihi a rubuce masana tarihi sun rika yin amfanin da maroka na kusa da zuri'ar Keita domin rubuta tarihin Soundiata Keita. Sai dai kuma a cikin rubuce-rubucen sun manta da irin nasarorin da ya gaza cimma. Kuma ana zargin marokan na zuri'ar Keita da tsayawa a karni daya tare da fifitashi a kan wasu aiyukan da ya yi. Wata cibiyar nazarin tarihi ta Kouroukan Fouga ta ce akwai sabani sosai tsakanin masana tarihi a game da tarihin Soundiata Keita.

 

Wadanda suka yi hidima wajen hada labarin: Tamara Wackernagel, Sidiki Doumbia da Philipp Sandner. Wannan bangare ne na shiri na musamman na Tushen Afirka "African Roots", shirin hadin gwiwa tsakanin tashar DW da Gidauniyar Gerda Henkel.

Sauti da bidiyo akan labarin