Sumame kan masu bore a Hong Kong
October 17, 2014Talla
Wannan sumamen da jami'an tsaron suka yi a lardin Mong Kok dai shi ne irinsa na uku a 'yan kwanakin da suka gabata a yunkurinsu na ganin masu zanga-zanga sun bar kan titunan da suka mamaye a birnin.
Hakan dai na zuwa ne bayan da shugaban yankin Leung Chun-ying ya nemi kashe rutar rikicin da yanki ke fuskanta ta hanyar farfado da tattuanawar da ta rushe a baya tsakanin gwamnatinsa da masu rajin tabbatar da dimokradiyya wanda galibinsu dalibai ne.