Sulhu kan batun gudanar da zabuka a Burkina Faso | Labarai | DW | 22.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sulhu kan batun gudanar da zabuka a Burkina Faso

'Yan takara a zaben shugaban kasar Burkina Faso da zai gudana a ranar 11 ga watan Octoba mai zuwa, sun rattaba hannu kan wata jarjejeniyar kauce wa tashe-tashen hankulla.

Hukumar sadawar kasar ce dai ta CSC ta dauki wannan mataki na shata yarjejeniyar da ke zaman wani babban alkawari ga 'yan kasar ta Burkina Faso, wanda kuma kafofin yada labaran kasar da ma kungiyoyin fararan hulla suka rattaba wa hannu a gaban shugaban kasar na rikon kwarya Michel Kafando. Sanin kowa ne dai zabuka a Afirka na a matsayin babban abun da ke kawo rarrabuwar kanu tsakanin al'umma, inda cikin jawabinta shugabar hukumar sadarwar kasar ta Burkina Faso Nathalie Somé, ta ce wannan yarjejeniya zata bada damar gudanar da zabe wanda babu tashin hankali a cikinsa wanda kuma kowa zai aminta da shi.