Sulhu da tsagerun Niger Delta ya fara aiki | Siyasa | DW | 21.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sulhu da tsagerun Niger Delta ya fara aiki

A Najeriya da alama an kama hanyar kai karshen rikicin yankin kasar mai arzikin man fetur inda gwamnatin da Kungiyar Avengers masu dauke da makamai suka sanar da tsagaiata wuta

Babu dai zato ba kuma tsammani rahotannin na tsagaita wuta a tsakanin kungiyar ta Avengers, mai farfasa bututun man fetur da gwamnatin kasar suka ce sun yanke hukunci na tsagaita wuta. Duk da cewar dai kama daga gwamnatin ta Abuja ya zuwa Kungiyar ta Avenegers sun ki fitowa fili su tabbatar da matakin da ke zaman ba bu zato.

wani jami'in kamfanin man fetur na kasar dai ya tabbatar wa DW cewar lallai an yi nasarar tabbatar da tsagaita wutar, a tsakanin bangarori biyun da ke kokari na ganin bayan junansu a farko. A cikin makon jiya ne dai aka bude tattaunawa a tsakanin karamin ministan man fetur Ibe Kachikwu da kuma yayan kungiyar. A wani abun da ke zaman cikon alkawarin wani taro a tsakanin gwamnonin yankin da kuma fadar ta Abuja makonni biyu baya.

Babu dai dalla-dallar abin da tsagaita wutar da kafafen yada labarai suka ce na zaman ta tsawon kwanaki 30 a karon farko. To sai dai kuma shi ma Mohammed Barkindo, sakatare janar mai jiran gado na Kungiyar OPEC ta masu arzikin man fetur da ya gana da shugaban kasar da ma ministan man dai, ya tabbatar da labarin da ke zaman mai dadi ga kasar.

Mohammed Barkindo Nigeria Afrika

Mohammed Barkindo, sakatare janar na kungiyar OPECRikicin na Avengers dai a baya ya yi nasarar gurgunta yawan man kasar da kusan kaso 60 cikin dari a cikin 'yan makonni. Akwai dai fatan yarjejeniyar za ta bude sabon fata ga kasar da ke da buri babba, amma kuma ke ganin ta leko tana shirin komawa sakamakon aiyyuka na tsagerun. Tun da farko dai Barkindo ya ce ya je fadar gwamnatin ta Abuja ne, da nufin godiya ga shugaban kasar da ya yi ruwa da tsaki wajen tabbatar da kasancewarsa sakatare na kungiyar, da ke zaman mafi tasiri a cikin harkar mai a duniya baki daya.

Abun jira a gani dai na zaman tasiri na yarjejeniyar da ke zuwa, dai dai lokacin da kungiyoyi daban-daban a yankin ke hankoron zama na halalin da ya kamaci tattaunawa da gwamnatin. Rikicin man dai ya kalli kasar ta Najeriya komawa daga matsayinta na farko a nahiyar Afirka ya zuwa ta biyu bayan Angola.

Sauti da bidiyo akan labarin