Sule Lamido tsohon gwamnan Jihar Jigawa da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya wanda ya rike madafun iko daga shekara ta 2007 zuwa 2015.
Sule Lamido ya kuma rike mukamin ministan harkokin wajen Najeriya daga shekarar 1999 zuwa shekara ta 2003 lokacin mulkin Olusegun Obasanjo, kuma Lamido yana cikin wadanda suka dade suna siyasa musamman lokacin Jamhuriya ta biyu da kuma Jamhuriya ta uku da ta rushe kafin mika mulki da shugaban gwamnatin farar hula.