1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bukatar sakin 'yan farar hula

Salissou Boukari LMJ
May 15, 2020

Sama da watanni biyu kenan da ake ci gaba da tsare wasu 'yan kungiyoyin fararen hula masu fafutukar kare hakkin dan Adam, a gidajen kaso daban-daban na Jamhuriyar Nijar, abin da ya janyo suka ga gwamnati.

https://p.dw.com/p/3cJ1a
Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou IssoufouHoto: AFP/I Sanogo

An dai kama 'yan kungiyoyin farar hular ne, bisa tuhumar shirya zanga-zangar da aka hana wadda a cikinta aka yi barna har da mutuwar mutane sakamakon wata gobara da ta tashi a ranar da aka yi zanga-zangar. Na baya-bayan nan dai daga cikin masu sukar lamirin gwamnatin ta Nijar da cewa tana take hakin fadar albarkacin baki da na gudanar da ayyuka kungiyoyin fararan hular, ita ce kungiyar ROTAB mai fafutukar ganin an yi adalci tare da ganin haske ga tsarin kasafin kudin  kasa da ma na kananan hukumomi.

Zabar wadanda ake saki

Kungiyar ta ROTAB dai ta nuna mamakinta da wani salo da ake yi na sallamar wasu a kyale wasu duk kuwa da cewa ana tuhumarsu ne da laifi guda. Kungiyar ta nuna takaicinta kan abin da ta ce mahukuntan na fakewa da dokar sa ido kan kafafen sada zumunta na zamani tana kama 'yan farar hular. 
A halin yanzu dai baya ga 'yan farar hular da suka hada da Maikol Zody da Moudi Moussa da kuma shugaban kungiyar Maluman Makaranta ta CYNACEB kuma mamba a kungiyar ROTAB Mounkaila Halidou da suke ci gaba da kasancewa a tsare, akwai kuma Maman Nassirou Mahamane Lawali wanda shi kuma dan kungiyar farar hula ta Croisade ne kuma mamba a kungiyar ROTAB Maradi da shi ma yanzu yake cikin gidan kaso.vSannan akwai Malla Tidjani da shi kuma ya ke gidan kaso na Daykaina sakamakon wasu kalamai da ya yi ta manhajar watsap kan batun Coronavirus.

Niger Ali Idrissa Koordinator ROTAB
Ali Idrissa shugaban kungiar ROTABHoto: DW/D. Köpp

In ani bi ta barawo......

Sai dai a cewar Sahnine Mahamadou mataimakin magatakardan kungiyar matasa ta PNDS Tarayya mai mulki, shi fa aiki na farar hulla idan har kana yinsa da gaskiya kowa ya sani. Da yake magana Oumarou Souley shugaban kungiyar farar hula ta FCR masu fafutikar nuna kishin kasa, cewa ya yi duk da cewa ba sa goyon bayan kungiyoyin da ke yi wa doka karan tsaye, amma kuma suna tausayawa abokannansu 'yan farar hular da ke tsare. A Halin yanzu dai duk da halin da ake ciki na annobar cutar coronavirus, za a iya cewa hankulan kungiyoyin fararan hular na Nijar, na kan batun nan na kame abokansu da aka yi da kuma batun almundahana da aka yi a ma'aikatar tsaro, inda kowa ya kasa kunne ya ji yadda za ta kaya.