1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu: Yarjejeniyar sulhu ta karshe

September 13, 2018

Salva Kiir da Riek Machar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karshe ta zaman lafiya a yakin da kasarsu ta shiga shekaru biyar da suka gabata.

https://p.dw.com/p/34mvd
Südsudan -  Riek Machar und  Salva Kiir
Hoto: Reuters/M. N. Abdallah

Shugaba Salva Kiir na kasar Sudan ta Kudu da jagoran tawayen kasar Riek Machar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karshe ta kawo karshen yaki da kasar ta sami kanta a ciki, a wani taron da aka yi a Addis Ababa na kasar Habasha, bayan tattaunawar makonni biyu.

Cikin watan jiya ne aka amince da samar da gwamnatin riko a kasar ta Sudan ta Kudu, inda za a maida Mr. Machar matsayinsa na mataimakin shugaban kasa. Sai dai duk da matsayin da bangarorin suka cimma a ranar Laraba (12.09.2018), da dama daga cikin masu kallon lamarin daga waje, na shakku kan nasarar dorewar hakan.

Jaririyar kasar ta fada yakin basasa ne a shekara ta 2013, bayan zargin yunkurin juyin mulki da Shugaba Salva Kiir ya yi wa Riek Machar, wato tsohon mataimakin nasa.