Sudan ta Kudu tana tattauna wa da Sudan | Labarai | DW | 05.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta Kudu tana tattauna wa da Sudan

Tun bayan girka gwamnatin hadin kan 'yan kasa a Sudan ta Kudu wannan shi ne karo na farko da ake irin wannan tattauna wa a birnin Khartum tsakanin bangarorin.

Sudan 5. Jahrestag Friedensabkommen

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da Shugaba Omar El Bechir na Sudan

Tawagar dai ta Sudan ta Kudu ta kumshi ministocin harkokin waje, da na tsaro, da ministan cikin gida da na man fetir, inda suke gana wa da takwarorinsu na Sudan a birnin Khartum, a wani mataki na neman walwale dumbun matsalolin da ke tsakanin su, da suka shafi batun 'yantar da kasar ta Sudan ta Kudu wanda ya wakana a shekara ta 2011.

Da yake magana yayin wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen kasar ta Sudan ta Kudu Deng Alor, ya ce ya iso da wani sako na Shugaba Salva Kiir ga Shugaba Omar al Bashir na Sudan, wanda ya yi kira da a gaggauta magance matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu.