1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu ta fara fidda mai ta Sudan

April 14, 2013

Ma'aikatar albarkatun man fetur ta kasar Sudan ta ce Sudan ta Kudu ta fara tura danyen mai zuwa Sudan din domin sayarwa ga abokan huldarta.

https://p.dw.com/p/18Feg
Sudan's President Omar Hassan al-Bashir (L) and his South Sudan counterpart Salva Kiir listen to their national anthems upon his arrival at the Juba Airport in South Sudan April 12, 2013. Bashir visits South Sudan on Friday for the first time since Africa's once-largest country split in 2011, raising hope the two long-time adversaries will take steps to establish peaceful co-existence. REUTERS/Andreea Campeanu (SOUTH SUDAN - Tags: POLITICS)
Umar al-Baschir Präsident Sudan Besuch im SüdsudanHoto: Reuters

Karamin minista a ma'aikatar Awad Abdul Fatah ne ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP a wannan Lahadin inda ya ce da yammacin jiya ne man ya fara isa Sudan to sai dai man da aka tura daga Sudan ta Kudun bai da yawa, hasali ma dai bai wuce wani mataki na gwaji ba.

Fara tura man dai na jiya ya biyo bayan cigaba da hakar danyen mai da aka yi kwanaki takwas din da su ka gabata a rijiyoyin man da ke Thar Jath bayan da aka rufe su kimanin shekara gudan da ta gabata bayan rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin kasashen biyu dangane da harajin da Sudan za ta rika karba a hannun Sudan ta Kudu saboda amfani da wani yanki na kasar ta wajen fidda man fetur din ta.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da shugaba Umar Hassan el-Bashir ya kai ziyara Sudan ta Kudu inda ya gana da shugaba Salva Kiir, lamarin da ya sa ake ganin hakan zai taimaka wajen farfado da dangantakar da ta yi tsami tsakanin bangarorin biyu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu