1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'amura na tabarbarewa a Sudan ta Kudu

Lateefa Mustapha Jaafar/ SBJuly 11, 2016

Fafatawar da aka yi tsakanin magoya bayan shugaban kasar Salva Kiir da kuma na mataimakinsa kana tsohon madugun 'yan tawaye Riek Machar, ta janyo asarara rayuka a birnin Juba.

https://p.dw.com/p/1JN5f
Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar
Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek MacharHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

A makon da ya gabata ne dai sabon fada ya kara barkewa tsakanin magoya bayan bangarorin biyu na Sudan ta Kudu. Mazauna yankin Jebel da ke makwabtaka da gidan mataimakin shugaban kasar Riek Machar sun tabbatar da cewa akwai karar harbe-harbe a yankin. Mai magana da yawun 'yan tawaye da ke goyon bayan Machar din James Gatdet ya zargi dakarun da ke biyayya ga Shugaba Salva Kiir da takalar fada, yayin da suma magoya bayan Shugaba Kiir din ke zargin tsofaffin 'yan tawayen da ke marawa Machar baya da fara tsokanar su. A hirarsa da tashar DW, shugaban shirin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu UNMISS Peter Shumann ya nuna damuwarsa kan yiwuwar ta'azzarar al'amura a kasar yana mai cewa:

Sojojin da ke marawa bangarori biyu baya na yakar juna
Sojojin da ke marawa bangarori biyu baya na yakar junaHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

"Yanayin da muke gani a yanzu abu ne mai tsoratarwa, munga abin da ya faru lokacin barkewar rikicin kasar a shekara ta 2013. Muna cikin faragabar ko lamura za su ta'azzara. Rahotannin da ke zuwar mana na halin da ake ciki a Juba, sunfi kusa da yi wuwar tabarbarewar al'amura da barkewar yaki maimakon lafawa."

Ita ma a nata bangaren wakiliyar DW a Juba, Patricia Huon, ta tabbatar da cewa ana ci gaba da jin karar harbe-harben bindigogi da tashin abubuwa masu fashewa, inda ta ce:

"Dubban fararen hula sun tsere domin neman mafaka a sansanin Majalisar Dinkin Duniya, su kansu jami'an na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu sun tabbatar da cewa an harba abubuwa masu fashewa a sansaninsu. An rufe tashohin sauka da tashin jiragen sama da hanyoyin mota na kasar. A yanzu motocin sojoji ne kadai ke yin zirga-zirga a Juba. Akwai gagagrumar fargabar cewa sabon yaki ka iya barkewa a Sudan ta Kudu."

Al'ummar Sudan ta Kudu na yin sabuwar kaura
Al'ummar Sudan ta Kudu na yin sabuwar kauraHoto: DW/L. Wagenknecht

Tuni dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa, inda ya bukaci bangarorin biyu da ma kasashen da ke makwabtaka da Sudan ta Kudun, da su tabbatar da ganin an shawo kan wannan sabon rikici ba tare da ya zama yaki ba. A cewar shugaban shirin Majalisar Dinkin Duniyar a Sudan ta Kudu, Peter Shumann tilas sai an dauki tsattsauran mataki a kan bangarorin biyu kafin a shawo kan matsalar da kasar ke ciki ya na mai cewa:

"Kamata ya yi a janye sojojin da ke birnin Juba baki daya. A ganina bangarorin biyu sun mayar da hankali ne kan yawan sojojin da za su kawo kasar. Salva kiir da Riek Machar ba za su taba taimakawa wajen kawo zaman lafiya a kasar ba. Muna bukatar sabuwar gwamnati da sabon tsari baki daya a Sudan ta Kudu."

Kawo yanzu dai duka bangarorin biyu na zargin juna da alhakin barkewar rikicin na baya-bayan nan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 300, sannan al'ummar ksar na ci gaba da zama cikin halin dar-dar.