Sudan ta Kudu: An sako ma′aikatan agaji da aka sace | Labarai | DW | 30.04.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta Kudu: An sako ma'aikatan agaji da aka sace

'Yan bindiga sun sako ma'aikatan agaji 10 na kungiyar Red Cross da aka yi garkuwa da su makon jiya a kudancin Sudan ta Kudu.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ma'aikatan agaji ke fuskantar barazanar kai hare-hare a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula a Sudan ta Kudu ba. Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin kasar ya lamushe rayukan ma'aikatan agaji 100 tun watan Disamban shekara ta 2013, a yanzu dai tuni aka wuce da ma'akatan da sukia kubuta a jitgin Red Cross zuwa Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu.