Sudan ta ce ba za ta kafa dakarun hadin guiwa don kare Sudan ta Kudu ba | Labarai | DW | 09.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta ce ba za ta kafa dakarun hadin guiwa don kare Sudan ta Kudu ba

Tun bayan barkewar rikicin Sudan ta Kudu wanda kuma ya yadu zuwa yankunanta masu arzikin mai, ake yi ta kira game da muhimmancin ba da kariya ga wadannan yankuna.

Rundunar sojan Sudan ta ce ba ta da niyar kafa wata rundunar hadin guiwa don taimaka wa Sudan ta Kudu ta kare yankunanta masu arzikin man fetir, sannan ta farfado da aikin hakar mai da ya gurgunce sakamakon yaki tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye. Kakakin sojan Sudan Kanal Khaled Sawarmi wanda ya yi wannan furucin, ya yi nuni da rashin nasara da aka samu a baya wajen hadin kai da Sudan ta Kudu, wadda ta balle daga Sudan a shekarar 2011. Tun bayan barkewar rikicin Sudan ta Kudu a ranar 15 ga watan Disamba wanda kuma ya yadu zuwa yankunanta masu arzikin mai, ake yi ta kira game da muhimmancin ba da kariya ga wadannan yankuna. A wannan Alhamis ma dakarun gwamnati sun ci gaba da gwabza fada a yunkurin sake kwace garin Bentiu daga hannun 'yan tawaye, yayin da fararen hula ke ci-gaba da tserewa daga fadan da ake yi a fadin kasar. Hakan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da alamu ke nuna cijewar tattaunawar samar da zaman lafiya a makwabciyar kasa wato Habasha.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh