Steinmeier ya yi fatan samun maslaha dangane tsarin mulkin EU | Labarai | DW | 12.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Steinmeier ya yi fatan samun maslaha dangane tsarin mulkin EU

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya nuna kyakkyawan fata dangane da cimma daidaito akan wani sabon kundin tsarin mulkin KTT. Steinmeier ya yi kira ga ´yan majalisar Turai dake wani zaman muhawwara akan makomar tsarin mulkin EU a Brussels da su manta da bambamce bambamce don a kai ga tudun dafawa. Shi kuwa shugaban hukumar kungiyar EU Jose Manuel Barroso kashedi yayi game da mawuyacin hali da za´a shiga ciki idan aka kasa cimma maslaha bisa manufa. Ya ce Turai zata yi rauni idan aka kasa cimma matsaya daya game da kundin tsarin mulkin. Taron kolin da shugabannin EU zasu yi a karshen makon gobe zai tattauna kan yadda za´a tinkari batun na kundin tsarin mulkin.