1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier ya fasa zuwa Ukraine

Abdoulaye Mamane Amadou Zainab Moh' Abubakar
October 20, 2022

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya soke ziyarar aiki a Ukraine bayan da Rasha ta kara tsananta luguden wuta kan manyan biranen kasar ciki har da Kiev.

https://p.dw.com/p/4IRyM
Deutschland | Bundespräsident Steinmeier am Telefon
Hoto: Guido Bergmann/Bundesregierung/dpa/picture alliance

Tun daga farko dai an sanar da cewa Shugaba Steinmeier zai yi tozali da takwaransa na Ukraine Volodymyr Selenskyj a birnin Kiev, sai dai kuma luguden wuta ba kakkautawa da Rasha ke yi a wasu manyan biranen Ukraine ciki har da Kiev sun haddasa dage tafiyar, ko da yake kakakin shugaban kasar da jakadan Ukraine a Jamus, sun bayyana a shafinsu na Twitter cewa kasashen Ukraine da Jamus na da anniyar tsara wata muhimmiyar ziyara nan da gaba, duk da yake ba su yi wani karin haske ba a kai. Ana sa ran shugabanin biyu na Jamus da Ukraine za su tattauna ta wayar tarho a wannan Alhamis.