Steinmeier a Afirka | Siyasa | DW | 15.02.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Steinmeier a Afirka

Ziyarar ministan harkokin wajen Jamus a Afirka

default

Minista Steinmeier tare da shugaban kasar Togo

Ministan harkokin wajen na Jamus yayi tattaki ne na kwanaki uku a yankin Afrika ta yamma. A bayan da ya shaidfar dfa wasan karshe na neman daukar kofin kwallon kafa na kasashen Afrika ranar Lahadi a Ghana, ya zarce zuwa Togo, inda a bayan shawarwarin sa na siyasa, ministan harkokin wajen na Jamus ya kuma yi bikin bude cibiyar yaki da cutukan yankuna masu zafi. Tashar karshe a ziyarar tasa a Afrika, ita ce Togo.


Wannan dai shine yadda aka karbi ministan harkokin waje, Frank Walter Steinmeier. Lokacin da ministan ya fito daga motar sa a garin Tsevie, ya taras da fiye da rabin mazauna wannan gari sun hallara suna jiran yi masa marhabin, tareda makada da mawaka da yan rawa. A can din yayi bikin bude cibiyar nazarin hanyoyin yaki da cutuka na yankuna masu zafi da aka gina tare da taimakon kudi daga nan Jamus. Ministan lafiya na Togo, har ma ya yi marhabnin da ministan daga Jamus ciin harshen Jamusanci:

Allah ya daukaki Jamus. Allah ya daukaki Togo, Allahy a daukaki hadin klan dake tsakanin Togo da Jamus.

Bude wannan cibiya, al'amari ne da ya baiwa masu masaukin ministan damar shirya gagarumin biki.

Ban yi tsammanin zan sami wnanan gagarumin tarba a matsayi na na Bajamushe, ko kuma taras da sha'awa mai tsanani ga harshen Jamusanci a nan ba. Dalibai fiye da dari takwas ne suke koyon harshe da tarihin Jamus ga kuma yan makaranta jasu tarin yawa dake koyon wannan harshe. Wannan kadai ya isa nunar da yadda dangantaka da tarihi take a tsakanin Jamus da Togo da kuma yadda zuriyar wnanan zamani take kokarin kiyaye wannan kyakkyawar dangantaka.

An yi shekaru masu yawa wani minista dfaga Jamus bai ziyarci kasar Togo ba, inda a bayan mulkin kama karya, tashin hankali mai tsanani ya barke a shekara ta 2005. A halin da ake ciki kwanciyar hankali ya samu a kasar, yayin da ta fara daukar matakai kan hanyar komawa ga democradiya. Steinmeier yace:

Tun daga watan Oktober, mun sami yamnayin da ba ma zabe kawai aka gudanar a Togo din ba, amma har mun ga alamu na amincewa da samun shawarwari tsakanin gwamnati da yan adawa, a kokarin gabatar d a wnai sabon tsari na zabe da kkarfafa matakai na sulhu a kasar aki daya.

A lokacin ganawa tare da shugaban kasar ta Togo, ministan harkokin waje Steinmeier ya tunatar da bukatar ci gaba kan hanyar sulhu da gyare-gyaren al'amuran kasa, saboda Togo har yanzu ba kasa ce dake bin tsari na shari'a da dokoki ba. Har ya zuwa yanzu babu soja ko dan sanda daya da aka gabatar dashi akotu saboda laifukan daruruwan yan kasar lokacin tashin hankalin shekara ta 2005. Duk da hakan, masu fafitikar kare hakkin yan Adam, kamar Emmanuel Atchade, ssuna iya baiyana ra'ayoyin su ba tare da tsoron abin da zai biyo baya ba.

Babban abin damuwar mu a yanzu shine rashin hukunta wadanda suke da laifin keta hakkin jama'a. Wadanda suka sha wahala daga matakan na keta hakkin yan Adam a kasar mu ya kamata su sami damar gabatar da kara gaban kotuna, a kuma biya su diyya.

Ko da shike Atchade bai yi ido hudu da ministan harkokin wajen na Jamus ba, amma ya nuna farin cikin ziyarar sa a Togo. Shina ministan a bayan da ya sadu da yan adawa a Togo, ya zarce zuwa Burkina Faso inda yayi wata yar gajeruwar ziyara ta yan awoyi kalilan. Kasar ta dade bata iya samar da isasshen abinci ga al'ummar ta, to amma yanzu an samun ci gaba sannu a hankali. Dangane da haka, ministan yace kol da shike Burkina Fasdo tana matukar sha'awar ci gaba da samun taimakon raya kasa daga Jamus, amma yana da muhimanci kasar ta dauki matakai na farfado da tsarin tattalin arzikin ta da kanta.

 • Kwanan wata 15.02.2008
 • Mawallafi Umaru Aliyu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/D7KA
 • Kwanan wata 15.02.2008
 • Mawallafi Umaru Aliyu
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/D7KA