1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tarwatsa masu zanga-zanga a kasar Spain iyaka da Faransa

Binta Aliyu Zurmi
November 12, 2019

'Yan sandan kasashen Faransa da Spain sun tarwatsa dandazon masu zanga-zanga da ke nuna kyamar sakamakon zaben 'yan majalisun dokoki da suka rufe babbar hanya da ke kan iyakar kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3StzY
Spanien Barcelona | Proteste  für die katalanische Unabhängigkeit
Hoto: Getty Images/AFP/P. Barrena

Wannan na zuwa ne biyo bayan rashin amincewa da zaben 'yan majalisun da ya gudana a karshen makon da ya gabata.'Yan sandan kasashen Faransa da Spain sun tarwatsa masu zanga-zanga da suka rufe babbar hanya da ke kan iyakar kasashen biyu.

Dubban masu zanga-zangar daga bangarorin biyu ne akai nasarar tarwatsa su dama bude hanyar ga matafiya. Rahotannin kafofin yada labarai, sun ce 'yan sandan kasar Faransa sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye  don tarwatsa masu gangamin, haka zalika sun kama mutum 18.

Firaministan Spaniya Pedro Sanchez da ya kasa samun rinjayen da zai bashi damar kafa gwamnati, ya bukaci al'ummar kasar da su bashi dama domin kawo karshen matsalolin siyasar da kasar ta ke fama da su.