1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati ta soki masu zanga-zanga a Spain

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
October 16, 2019

Hukumomi a Spain sun yi kakkausar suka game da barkewar bore da zanga-zanga a yankin Kataloniya biyo bayan jama'a sun fito nuna rashin jin dadinsu da matakin kotu na kargame kusoshin 'yan awaren yankin gidan yari.

https://p.dw.com/p/3RMZR
Spanien Barcelona | Demonstration zum Nationalfeiertag
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/J. Boixareu

Wata sanarwa da gwamnatin Spain ta fitar ta caccaki shugabannin 'yan awaren Kataloniya da ke neman cin gashin kan yankin, tare da bayyana su a matsayin wasu 'yan tsirarun da ke son haddasa fitina da tarwatsa hadin kan yankin ta hanyar amfani da hanyoyin tunzura jama'a da su gudanar da tashe-tashen hankula.

A baya an sha yin arangama tsakanin jami'an tsaro da masu bore da zanga-zanga a wasu sassan kasar. Sa'o'i bayan da wata kotu a kasar ta yanke hukuncin shekaru tara zuwa 13 a gidan kurkuku ga wasu jiga-jigan 'yan awaren yankin na Kataloniya, jama'a a yankin Kataloniya sun yi tir da matakin kotu.