1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soyinka: A tuntubi 'yan Biafra don yin sulhu

Abdul-Raheem Hassan/ MABDecember 9, 2015

Wole Soyinka ya bukaci gwamnatin Najeriya ta sauya salon tinkarar masu yunkurin kafa kasar Biafra idan ta na son kawo karshen wannan rikici cikin ruwan sanyi.

https://p.dw.com/p/1HKwe
Wole Soyinka
Hoto: Andreas Rentz/Getty Images

Fitaccen marubucin adabin nan na Najeriya Wole Soyinka ya gargadi gwamnatin kasar kan illar da ke akwai wajen yin amfani da karfi kan masu rajin kafa kasar Biafra. Cikin wata hira da ya yi da wata kafar watsa labarai, Soyinka mai shekaru 81 a duniya ya bukaci gwamnatin Buhari da ta yi amfani da hanyoyin lumana wajen kawo karshen yunkurin aware a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya.

A makonnin da suka gabata ne dai masu fafutukar ballewa suka gudanar da zanga-zanga domin tilasta wa gwamnati sako shugaban Rediyo nan, na gagwarmayar samar da 'yantaciyar Biafra, Nnamdi Kanu. Sannan kuma sun bukaci a basu damar kafa kasa ta kabilar Nyamurai zalla, shekaru 45 bayan yakin basasa da aka fuskanta a Najeriya sakamakon neman ballewa.

Wole Soyinka ya na ganin cewar akwai bukatar sauraran koken 'yan awaren da kunnuwan basira, don magance abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya.