1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Yawan wanda suka rasu ya karu

Ramatu Garba Baba
October 16, 2017

Sama da mutane 270 suka halaka a sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a kasar, wasu daruruwa kuwa sun sami rauni a harin ta'addancin da ya kasance mafi muni a tarihin Somaliya.

https://p.dw.com/p/2lu6N
Somalia Mehr als 260 Tote nach Doppel-Anschlag in Mogadischu
Hoto: Reuters/F. Omar

Alkaluman mamata ya ci gaba da karuwa  tun bayan kazamin harin da aka kai da wata babbar mota makare da bam a kofar shiga wani otal mai cunkoson jama'a a birnin Mogadishu. Baya ga 'yan kasar Somaliya da wannan lamari ya shafa, wasu 'yan kasashen ketare ma sun shiga jerin wanda suka raunata ko ma suka rasu sakamakon harin. Wata mata mai suna Ruun Abdi ta ce mai gidanta wanda sojan Amirka wanda ya gamu da ajalinsa a harin inda ta ke cewar ''mutumin kirki ne wanda ya ke aiki haikan''.

Yayin da al'ummar kasar ke cigaba da yin zaman makoki na wanda aka rasa da kuma jinyar fiye da mutane 500 da suka jikkata, shugaban Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo ya nemi hadin kan 'yan kasar don ganin an kawo karshen kungiyar Al-Shabaab da ke gwagwarmaya da makamai a kasar wadda a cewarsa ita ce ta kai harin duk kuwa da cewar kungiyar ba ta bayyana cewar ita ce ta kai ba.

Wannan harin na ba-za-ta dai ya sa murna ta koma ciki a kasar da al'ummarta ke murnar farfadowa daga cikin kuncin da ta sami kanta sanadiyar yawaitar hare-haren 'yan bindigar Al-Shabbab, yayin da a share guda hukumomi ke kokari wajen ganin sun tabbbatar da dorewar zaman lafiya.