1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya ta yi nasara a kan Kenya a kotu

Mouhamadou Awal Balarabe
October 12, 2021

Kotun kasa da kasa ICJ da ke birnin The Hague ta bai wa Somaliya kaso mafi tsoka na yankin tekun Indiya mai arzikin kifi da yiwuwar arzikin iskar gas da kasar Kenya ta yi ikirarin cewa mallakinta ne.

https://p.dw.com/p/41b3S
Den Haag Internationaler Gerichtshof IGH
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Cikin hukuncin da ta yanke a wannan Talata, kotun ta ICJ ta ce babu iyakar teku da aka amince da ita tsakanin kasashen biyu a baya, amma ta shata wata sabuwar iyaka kusa da inda Somaliya ke ikirarin mallaka, yayin da Kenya za ta ci gaba da rike wani bangare na ruwan da ke tsakanin kasashen biyu.

Wannan hukunci na babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya zai kawo karshen takaddamar kan iyaka da aka fara a shekarar 2014 tsakanin Kenya da Somaliya, wacce kuma ke kara dagula alakar da ke tsakanin makwabtan biyu na gabashin Afirka.

Tun Kafin yanke hukuncin, Kenya ta zargi kotun da fifiko kuma tuni ta nuna cewa ba ta amince da hukuncin Kotun ba. Sai dai hukuncin kotun kasa da kasa na kasancewa na karshe, amma ba ta da wata hanyar tilasta wa kasashen aiwatar da su.