1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Mutane miliyan biyar na fiskantar yunwa

Yusuf BalaSeptember 20, 2016

Kananan yara su suka fi fiskantar barazana ta wannan rashin abinci da ma yiwuwar mutuwa a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/1K5dm
Symbolbild Lebensmittelmangel
Baya ga fari ga tashe-tashen hankula a Somaliya sun addabi al'ummaHoto: Getty Images

Adadin al'ummar kasar Somaliya da ba su da ishashshen abin da za su ci ya karu zuwa miliyan biyar, ko kuma duk mutane hudu daga cikin al'ummar kasar goma na fiskantar wannan matsala, saboda karancin ruwan sama da aka fiskanta a wannan kasa a cewar MDD a ranar Talatan nan, wanda a cewarta yara kanana su ne rayuwarsu ke cikin hadari na rashin lafiya ko ma mutuwa.

Majalisar har ila yau ta kara da cewa wannan babban abin tashin hankali ne duba da yadda a yanzu duniya ke fama da matsaloli na fari da ambaliyar ruwa da rikice-rikice ga karuwar 'yan gudun hijira.

Dubban 'yan gudun hijira ne cikin wannan shekara sun koma kasar ta Somaliya daga sansanin Dadaab, bayan da kasar Kenya ta bayyana shirin rufe sansani baki daya a watan Nuwamba.