Soma zaman makoki na kwanaki uku a Nijar
February 19, 2015Talla
A lokacin da yake magana kan wannan lamar,i kakakin gwamnatin ta Nijar kuma ministan shari'ar kasar Marou Amadou, ya ce za'a gudanar da bincike domin gano jirgi ko kuma jiragen da suka yi wannan danyan aiki.
An dai fara makoki na kwanaki uku a fadin kasar ta Nijar daga yau Alhamis domin tunawa da marigayan wadanda aka kashe yayin da suka taru kusa da wani masallaci sakamakon wani rishi da suka samu a wannan gari, inda harin ya yi sanadiyar rasuwar mutane a kalla 36 tare kuma da jikkata wasu a kalla 20. Sai dai tuni mazauna wannan gari suka tabbatar cewa jiragen na Najeriya ne. Ko ma dai minene bincike ne kawai zai tabbatar da hakan, saboda gwamnati ta ce za iya kokarin tabbatar da zahirin abin da ya faru.