Soma zaben EU a Holland da Birtaniya | Labarai | DW | 23.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Soma zaben EU a Holland da Birtaniya

Al'ummomin kasashen Holland da Birtaniya sun soma a wannan Alhamis gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin Turai wanda za a kwashe kwanaki uku ana gudanar da shi daga wannan kasa zuwa waccan a cikin kasashe mambobin EU.

Mutane kimanin miliyan 400 masu rijistan zabe a kasashen 28 na Turai za su zabi 'yan majalisar dokokin Turai guda 751. An dai bude runfunan zaben ne tun da misalin karfe biyar da rabi agogon JMT a kasar ta Hollande mai kujeru 26 a majalisar Turan.

Alamu na nuni da cewa jam'iyyar FVD mai akidar adawa da Kungiyar Tarayyar Turai da kuma kyamar 'yan gudun hijira ta Thierry Baudet dan shekaru 36 ce za ta zo a matsayi na daya a zaben. 

A Birtaniya kuma mai shirye-shiryen ficewa daga Kungiyar ta EU  da kuma ke da kujeru 73 a cikin majalisar Turan an bude runfunan zaben ne a karfe shida agogon GMT.