Sokoto: Tambuwal ya lashe zaben gwamna | Labarai | DW | 24.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sokoto: Tambuwal ya lashe zaben gwamna

Dan takarar jami'iyyar PDP kuma gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya lashe zaben Sokoto a gaban dan takarar jam'iyyar APC Ahmed Aliyu.

Hukumar zaben dai ta bayyana sakamakon wanda ke nuna cewar gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya lashe zaben Sokoto da kuri'u 512,002 yayin da ,Ahmed Aliyu na jam'iyyar APC. ya samu kuri'u 511,660.