Sojojin Ukraine na kara samun galaba. | Labarai | DW | 15.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Ukraine na kara samun galaba.

Dakarun Sojan Ukraine dake fafatawa da 'yan awaren gabacin kasar, na ci-gaba da samun galaba tare da amshe wasu muhimman garuruwa dake yankin.

Dakarun na Sojan Ukraine, sun samu karbe wata hanya mai muhimmanci dake tsakanin 'yan Awaran birnin Lougansk zuwa iyaka da Rasha a jiya Alhamis (14.08.2014), inda hakan ya basu damar tare hanyar da jerin motocin kayayakin agajin da Rasha ta aika ya zuwa gabacin na Ukraine zai bi.

Dangane da gurgusowar dakarun sojan kasar ta Ukraine, da kuma kara samun mace-macen da ake na al'umma sakamakon fadan dake wakana a tsakiyar birnin Donetsk, biyu daga cikin jagororin 'yan awaran sun mika takardar murabus din su a jiya Alhamis.

Sai dai daga nata bangare Rasha ta fara jibge tankoki a yau din nan kusa da iyakar kasar da Ukraine, abun da Ukraine din ke zargin cewa Rashan na famar amfani da kai kayan agajin ne don mamayar gabacin kasar. Daga nata bangare, Amirka ta yi kira ga hukumomin Ukraine, da suyi sassauci domin takaita mace-macen fararen hulla.

Mawallafi : Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Aboubakar