1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hari Siriya

Ramatu Garba Baba
November 19, 2022

Sojojin Siriya akalla 4 ne suka mutu a sakamakon wani hari da ake zargin rundunar sojojin Isra'ila da kai wa kan yankunan bakin tekun kasar.

https://p.dw.com/p/4JlpG
Sojojin Siriya 4 sun mutu a harin Isra'ilaHoto: Getty Images/AFP/G. Ourfalian

Wani hari ta sama da jiragen rundunar sojin Isra'ila suka kai a yankunan tsakiya da bakin tekun ruwan Siriya, ya hallaka jami'an sojojin Siriyan hudu tare da raunata soja guda. Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights ta Britaniya da ke sa ido kan kare hakkin dan adam a Siriyan ta ce, an yi ta jin karar abubuwan fashewa a gabar tekun da kuma yankunan Hama da Homs ba tare da ta yi karin bayani ba kan harin na safiyar wannan Asabar ba.

Kawo yanzu babu wata sanarwa daga bangaren Isra'ila kan harin, sai dai a baya, rahotanni sun sha tabbatar da hare-haren rundunar sojojin Isra'ilan a Siriya a wani yunkuri da ake zaton tana yi don ganin ta hana tasirin kungiyoyi masu gwagwarmaya da ke da alaka da gwamnatin  Iran.