1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin sa ido na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Golan

November 6, 2012

Tun bayan yakin da aka gobza tsakanin Isra'ila da kasashen larabawa,Majalisar Dinkin Duniya ta haranta ayukan soji a filin.

https://p.dw.com/p/16dNd
Hoto: AP

Rahotani daga birnin Kudus,sun rawaito cewar a wannan Littanin ne, wata motar yakin Isra'ila ta fuskanci aman wuta daga bangaren dakarun Siriya da suka shiga yankin Golan. Duk da dai babu wani bayanin dake tabbatar da ko wadanda ke ciki sun samu raunika,Isra'ila ta ce a shirye ta ke ta maida martani ga dakarun na Siriya nan bada jimawa ba a matsayin tsokanar da ake yawaita mata.
Dama dai tun a karshen makon nan ne Isra'ila ta shigar da kara a tawagar sa'ido ta majalisar dinkin duniya da ke yankin na Golan bayan da ta ce wasu tankokin yakin Siriyar sun kutsa a yankin da aka haratawa ayukan soji tun bayan yakin da aka gobza tsakanin Isra'ila da kasahen larabawa a shekara ta 1973.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi