Sojojin Nijar sun mutu a harin ta′addanci | Labarai | DW | 02.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Nijar sun mutu a harin ta'addanci

Gwamnatin Jamhguriyar Nijar ta tabbatar da mutuwar sojoji 18 a yayin da wasu hudu suka bata sakamakon harin ta'addancin da 'yan bindiga suka kai kan wani bariki a yankin Tillaberi.

Lamarin ya faru ne a tsakiyar ranar jiya, inda wasu motocin biyu shake da bama-bamai su tarwatse a cikin barikin sojan, kafin daga bisani maharan da suka yi kawanya su bude wuta.

A wata sanarwar da ta fitar a yau din nan, ma'aikatar tsaron kasar ta Nijar ta ce duk da hasarar sojojinta 18, askarawan kasar tare da taimakon rundunar sojan sama na Amirka da Faransa, sun fatattaki 'yan ta'addan tare da hallaka wasu da dama.

Yankin dai na yammacin Nijar mai makwabtaka da Mali da Burkina Faso na fuskantar hare-haren 'yan ta'adda a kai-a kai tare da zama sanadiyar mutuwa ta sojojin kasar da dama.