1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Boko Harm su kai hari a barikin soji a Nijar

Abdourahamane Hassane
March 17, 2020

Gwamnatin Nijar ta ce sojojinta sun kashe mayakan Boko Haram guda 50 a Toumour da ke a kudu maso gabashin kasar a Diffa a wani fadan da aka gwabza.

https://p.dw.com/p/3ZYYx
Symbolbilder Niger Armee
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Gwamnatin Nijar ta ce mayakan Boko Haram dauke da manyan makamai a cikin motocin yaki kusan 20 sun kai hari a kan barakin soji  na Toumour da ke cikin Jihar Diffa, sai dai ta ce sun kwashi kashinsu a hannu. A farkon wanan wata hare-haren da mayakan na Boko Haram suka kai a Chetima Wangou cikin Jihar ta Diffa sun yi sandiyyar mutuwar sojojin gwamatin takwas kana wasu uku suka yi batan dabo.