Sojojin Najeriya sun rufe ofishin agaji | Labarai | DW | 19.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya sun rufe ofishin agaji

Bayanani daga yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun tabbatar da cewa sojojin kasar sun afka wa wata cibiyar agaji tare da dakatar da harkokin da take gudanarwa na jin kai.

An rufe ofishin kungiyar Action Against Hunger ne da ke Maiduguri ba tare wasu cikakkun bayanai ba. Kungiyar ta fitar da wani rahoto bayan da mayakan Boko Haram suka sace musu ma'aikata.

Wani daga cikin ma'aikatan kungiyar, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa sojojin sun isa ofishin nasu ne tare da korar kowa da kowa; kuma suka ce umurni ne da ya zo musu daga sama.

A jiya Laraba ne dai sojin suka tada ofishin kungiyar ta Action Against Hunger wanda har yanzu suke rufe da offishin. 

Kungiyar dai na daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aikin agaji a yankin arewa maso gabashin Najeriya.