Sojojin Najeriya sun fatataki mayakan Boko Haram | Labarai | DW | 19.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya sun fatataki mayakan Boko Haram

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da kubtar da wasu mutane 195 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su ya yin wani samame da suka Kai.

Bayan ma mutanen 195, rundunar sojojin ta Najeriya ta sanar da samun wasu manyan motoci biyu, da babura 180, da kekuna 750 wadanda mayakan ke amfani da su ya yin da suke kai hare-haren su na ta'addanci. Mai magana da yawun rundunar sojojin ta Najeriya Kanar Sani Usman cikin sanarwar ya kara da cewa sojojin na su sun hallaka mayakan kungiyar ta Boko Haram da dama. A makon da ya gabata ma dai sojojin Kamarun sun kai wani samame ga wata maboyar mayakan na Boko Haram cikin Najeriya.