1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Najeriya sun dakile harin ta'addanci

Ramatu Garba Baba
April 27, 2018

Sanarwa da rundunar tsaron Najeriya ta fitar, ta ce ta yi nasarar dakile wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi yunkurin kai wa kan mazauna birnin Maiduguri da ke jahar Borno a daren jiya Alhamis.

https://p.dw.com/p/2wlaF
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Sanarwar ta ci gaba da cewa 'yan sanda da aka ajiye a wannan yankin ne suka mayar da martani a daidai lokacin da mayakan suka soma barin wuta a garin. Mazauna yankin sun bayar da labarin yanda suka yi ta jin karar bindigogi, lamarin da ya matukar haifar da fargaba a tsakanin al'umma, tare da tilastwa tarin mutane barin gidajensu.

Wannan shi ne karo na biyu da 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya ke yunkurin kai hari ba tare da samun nasara ba a jahar.Babu asarar rai a sanadiyar artabun inji sanarwar.

Mutane fiye da dubu talatin ne suka rasa rayukansu tun bayan da kungiyar ta Boko Haram ta kaddamar da ayyukanta a Najeriya a shekarar 2009.