Sojojin MDD sun yi ta′asa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Siyasa | DW | 13.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojojin MDD sun yi ta'asa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Jagoran rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato MINUSCA Babacar Gaye ya yi murabus bayan zargin da aka yi wa jami'an rundunar na cin zarafin yara kanana.

Jami'in yayi murabus ne sakamakon matsin lambar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, bayan zargin da aka yi wa jami'an rundunar ta MINUSCA na cin zarafin yara kanana ta hanyar yi musu fyade.

Wannan sanarwa ta ajiye aiki da Janar Babacar Gaye dan kimanin shekaru 64 ya bayyana, ta biyo bayan wani rahoton da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta wallafa wanda yanzu aka soma yin bincike a kansa.

A cikin rahoton kungioyar ta ce jami'an rundunar kiyaye zaman lafiyar na MINUSCA a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun yi wa wata yarinya fyade tare da kashe wani matashi mai shekaru 16, tare da mahaifinsa a lokacin wani sintirin da suka kaddamar a farkon wannan wata a unguwar PK5 da ke birnin Bangui, wacce galibi musulmi suka fi yawa a ciki.

Akalla dai sojojin na MINUSCA a lokacin wannan farmaki sun kashe mutane biyar, amma kuma su ma an kashe musu mutum daya yayin da wasu da dama suka jikkata.

Jami'an rundunar dai sun kai wannan samame ne a kokarin da suka yi na kama wani jagoran tsohuwar kungiyar yan tawaye ta SELEKA a unguwar ta PK5. A lokacin wani taron manema labarai da ya yi, babban sakataran Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya ce shi ne ya tilasta wa Babacar Gaye yin marabus saboda wannan abun kumya da jami'an rundunar suka tafka.

Jonathan Pedneault, wani babban jami'i da ke yin aiki da kungiyar Amnesty a birnin Bangui yace:

"Ya ce mu dai abinda muke bukata shine a gaggauta yin bincike a kan rundunar ta MUNISCA, sannan ya kamata a ce jami'an sojojin na rundunar wadanda suka aikata wannan ta'asa sun gana da masu binciken, sannan muna bukatar kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty reshen kasar ta je unguwar ta PK5 a Bangui domin saduwa da jama'ar don jin ta bakinsu".

Französische Soldaten in der Zentralafrikanischen Republik

An zargi sojojin MINUSCA da laifin yi wa yara fyade

Duk da wannan bukata ta yin binciken ita ma Majalisar Dinkin Duniya ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa domin bincika lamarin. Kakakin majalisar, Stephane Dujaric, ya ce ana zargin jaman rundunar ta MUNISCA a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da aikata laifuka a cikinsu 11 na yin fayde a kan kanana yara, kuma an shirya kwamitin sulhu na Maajalisar Dinkin Duniya zai yi wani zaman taron gaggawa domin tattauna wannan batu.

Thierry Vicoulon na kungiyar CRISI Group ya ce lamarin na tada hankali:

"Ya ce watakila ma zarge-zargen da ake yi wa jami'an rundunar ta MUNISCA ya wuce abinda ake tsamani a sakamakon harin da suka kai a unguwar PK5 da ke Bangui, wacce ba ta yi nasara ba saboda basu kama wanda suka je nema ba. Ina tsamanin baban dalilan yin wannan ta'asa ba su ne kawai suka sa janar Babacar Gaye yin marabus ba, akwai matsaloli na rashin jituwa ma da ke tsakanin 'ya'yan rundunar ta MUNISCA.

Janar Babacar Gaye wanda ya rike mukamai da dama na sojoaa kasar Senagal, a ciki har da na rundunar sojojin kasar daga shekarun 2000 har zuwa shekara 2013 lokacin da aka cireshi daga matsayin na da hannu a cikin hadarin jirgin ruwan da ya auku a Senegal a shekarun 2002 wato hadarin JOOLA wanda a ciki kusan mutane dubu biyu suka mutu.

Sauti da bidiyo akan labarin