Sojojin Masar sun sanya baki a rikicin ƙasar | Labarai | DW | 01.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Masar sun sanya baki a rikicin ƙasar

kasancewar zanga-zangar adawa da gwamnatin Mursi na Masar na ci gaba da rincaɓewa, sojoji sun baiwa jagororin siyasar ƙasar sao'i 48 su ɗauki matakin da zai kawo maslaha

Sakamakon gagarumar zanga-zangar da ke adawa da shugaba Muhammed Mursi, dakarun sojin Masar sun baiwa jagororin siyasar ƙasar wa'adin shawo kan wannan rikicin, inda manyan hafsoshin sojin suka ce wajibi ne a sami maslaha nan da sao'i 48, kuma sun ce dole ne a yi la'akari da buƙatun 'yan ƙasa.

A tsakanin 'yan kwanakin baya-bayan nan ne zanga-zangar ta daɗa rincaɓewa, kuma bayan wannan wa'adi da rundunar sojin ta bayar, Mursi ya shiga ganawa da hafsoshin

Da ranan nan ne a birnin Alƙahira masu zanga-zanga suka kai hari kan Hedkwatar Jamiyyar 'yan uwa musulmi wato Muslim Brotherhood, wacce ta fi kusanci da shugaba Mursi.

Su dai waɗannan masu boren sun ce sun baiwa Mursi wa'adin nan zuwa yammacin Talata ya yi murabus, huɗu daga cikin ministocinsa sun riga sun miƙa takardun murabus ɗinsu.

Masu fashin baki dai na zargin Mursi da daukaka manufofin jamiyyarsa ta 'yan uwa musulmi kan buƙatun 'yan ƙasa.

Haka nan kuma sun ce matsalolin tattalin arziƙi da zamantakewar ƙasar ko ɗaya ba su sauya ba bacin kasancewarsa a muƙami na tsawon shekara guda cif yanzu, kuma a dalilin haka, mulkinsa ya rasa sahihanci a idon 'yan ƙasa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal balarabe