Sojojin Kwango sun kwace gari mai mahimmanci
October 30, 2013Dakarun na gwamnatin Kwango dai sun kwace garin Bunagana na gabashin kasar daga hannun kungiyar 'yan tawaye ta M23. Kakakin gwamnatin kasar Lambert Mende, ya bayyana haka wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, inda ya ce an yi musanyan wuta tun da sanyin safiyar wannan Laraba, kafin fatattakar 'yan tawayen.
Kakakin gwamnati ya tabbatar da kwace garin da ke zama mafi girma a hannun 'yan tawayen, wanda ke kan iyaka da kasar Yuganda. Wani jami'in sojan Majalisar Dinkin Duniya ya gaskata labarin kwace garin na Bunagana da ke da nisan kilo-mita 80 a arewacin birnin Goma.
Majalisar Dinkin Duniya na zargin 'yan tawayen na M23 da aikata laifukan yaki cikin gabashin kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman