Sojojin Kungiyar AU da dama sun halaka a Somaliya | Labarai | DW | 02.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Kungiyar AU da dama sun halaka a Somaliya

Sojojin kasar Yuganda mambobin rundunar zaman lafiya ta Tarayyar Afrika ta Amisom kimanin 50 sun halaka a cikin wani hari da Kungiyar Shebaab ta kaddamar a barikinsu a jiya Talata.

Sojojin kasar Yuganda mambobin rundunar zaman lafiya ta Kungiyar Tarayyar Afirka a kasar Somaliya ta Amison akalla 50 ne ake kyautata zaton sun halaka a kasar Somaliya a lokacin wani hari da mayakan Kungiyar Shebaab suka kaddama a cibiyar sojojin ta Jalane da ke a kudancin kasar a ranar Talatar Jiya.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wanda ya ruwaito wannan labari ya ce wata wasika da aka aika wa jami'an diplomasiyya a kasar ta Somaliya ne ta tabbatar da abkuwar lamarin inda ya ce mayakan kungiyar Shebaab din sun yi nasarar kwace barikin sojojin rundunar zaman lafiyar ta Amisom da ke a garin na Jalane kafin daga bisani sojojin kawancan sun sake karbeta a yammacin jiya Talata.

Kawo yanzu sojojin rundunar ta Amisom kimanin 100 ba a da labarinsu tun bayan abkuwar harin wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar Somaliya.