Sojojin Jamus za su bar Mali a 2024
December 28, 2022Sannu a hankali dai aikin dakarun Jamus ta Bundeswehr a kasar Mali da ke yammacin Afirka yana kara shiga cikin hadari, sakamakon janyewar abokan hulda na kasa da kasa da rashin samun izinin shawagin jiragen sama da rashin iya sarrafa marasa matuka. Amma duk da haka, a yayin ziyarar Kirsimeti da ta kai wa sojojin Jamus a Bamako a tsakiyar watan Disamba, ministar tsaron kasar Christine Lambrecht ta yi amfani da kalmomin da suka dace a wata tattaunawa da ta yi da takwararta Sadio Camara wajen bayyana cewar: Bundeswehr za ta ci gaba da zama a Mali har zuwa shekara ta 2024 idan an cika wasu sharudda, misali gudanar da zabukan ‘yan majalisar dokokin kasar da aka sha dagewa amma kuma a yanzu aka tsayar da gudanar da zaben a watan Fabrairun shekarar 2024. Tsawaita wa'adin har sai sojojin sun janye yana ba da damar yiwuwar sake ci gaba da aiki a Mali, in ji Ulf Laessing shugaban shirin yankin Sahel na gidauniyar Konrad Adenauer a Bamako.
Sai dai dai a cewar dan jaridar kasa da kasa na Nijar kuma marubuci Sadiq Abba da sauran rina a kaba dangane da cimma wannan buri na gudanar da zabe a watan Febrairun shekarar 2024 bisa la'akari da halin da kasar take ciki. A watan Mayun shekarar 2024 ne tawagar Bundeswehr mai yawan sojoji 1400 za ta kawo karshen zamanta bayan shekaru 10 na zama a kasar ta Sahel cikin tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA. Dakarun na Jamus za su shiga cikin rukunin horar da sojoji na musamman a Nijar nan gaba, in ji ministar tsaron kasar Lambrecht a ziyarar da ta kai makwabciyar kasar. Sabuwar kawancen tarayyar Turai da Nijar da ke fama da talauci na da nufin karfafa yaki da masu jihadi a yankin. Tawagar mai suna EUMPM Niger, za ta taimaka wajen gina cibiyar horaswa da bataliyar sadarwa da bayar da umarni, a cewar EU. Da farko an shirya zai kai shekaru uku. Euro miliyan 27.3 shi ne kudin hadin gwiwar tarayyar Turai.