Sojojin Isra´ila 57 sun jikata a wani harin roka daga Zirin Gaza | Labarai | DW | 11.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Isra´ila 57 sun jikata a wani harin roka daga Zirin Gaza

Wani makami mai linzami da sojojin sa kai na Falasdinawa suka harba daga Zirin Gaza ya afka kan wani sansanin sojin Isra´ila inda ya jiwa akalla sojoji 57 rauni. Harin wanda shi ne mafi muni a cikin watanni da dama zai kara matsin lamba akan gwamnatin Isra´ila da ta nemo hanyoyin kawo karshen kaiwa Isra´ila hare haren rokoki. A cikin wata sanarwa da suka bayar a birnin Gaza, baradan kungiyar Al-Quds bangaren soji na kungiyar Jihadin Islami sun yi ikirarin kai harin. Kungiyar wadda ke da alhakin kai hare haren rokoki daga Zirin Gaza zuwa Isra´ila ta ce zata yi wani taron manema labarai a wani lokaci yau din nan. A cikin makon jiya FM Ehud Olmert ya ce ba tare da wani jinkiri ko nuna tausayawa ba Isra´ila zata kaddamar da hare haren daukar fansa akan duk wani harin roka da za´a kai mata daga Zirin Gaza, wanda ke karkashin ikon Hamas.