Sojojin Iraki: Kokarin kwato Ramadi daga IS | Labarai | DW | 26.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Iraki: Kokarin kwato Ramadi daga IS

Duk da bama-baman da mayaka suka dana a wurare da dama, sojojin na kara dannawa a kokarin su na kwace wasu wurare na gwamnati da mayakan suka buya.

Dakarun sojan Iraki na ci gaba da danna wa sannu zuwa unguwa ta karshe ta birnin Ramadi inda mayakan kungiyar IS suka rage. Sai dai sojojin na fuskantar babban kalubale dangane da dumbun bama-baman da 'yan ta'addan suka dana a wurare da dama na birnin, sannan kuma akwai masu harbin dauki dai-dai da suka labe a wasu wurare.

A yanzu dai sojojin sun ki bada wani wa'adi na samamen karshe da za su kai wa mayakan na IS. Tuni dai ake kallon karbar wannan birni na Ramadi a matsayin wata babbar nasara ga dakarun sojan na Iraki. Jami'an yaki da ta'addanci na kasar ta na a kewayan wasu tarin ginene na gwamnati inda mayakan suke ciki, kuma harbe-harbe ta sama sun taimaka wajan tarwatsa bama-baman da mayakan suka dasa a cikin gidaje. Matakin sojojin na Iraki a wannan yaki, shi ne na kaucewa hallaka rayukan wadanda ba su ji ba su gani ba.