Sojojin Iraƙi sun shiga Tikrit bayan wani gumurzu | Labarai | DW | 12.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Iraƙi sun shiga Tikrit bayan wani gumurzu

Sojojin sun kutsa kai a birnin na Tikrit bayan wani gaggarumin farmakin da suka ƙaddamar na tsawon kwanaki goma.

Sojojin waɗanda suka haɗa da 'yan sanda da sauran dakarun sa kai galibi yan Shi'a sun yi nasarar ƙwace mafi yawanci unguwar Qadisiyah da ke a arewacin birnin.Sai dai wani babban jami'in rundunar sojojin Iraƙin ya ce har yanzu da sauran rina a kaba,saboda yadda ya ce suke cin karo da masu harbi ɗauki ɗaya-ɗaya da ke ɓoye a kan rufin gidaje.

A cikin watan Yuni da ya wucce ne mayaƙan sa kai masu jihadi na Ƙungiyar IS suka karɓe iko da birnin na Tikrit da ke a yankin arewaci