Sojojin Faransa sun kashe 'yan kishin Islama 60 a Mali
January 14, 2013Wadanda suka shedar wa idanununsu sun ce 'yan kishin Islama sama da 60 sun mutu a cikin luguden wutan da sojojin na Faransa suka yi a garin Gao. Ita kuma gwamnatin Jamus tana ba da taimako ga sojojin na Faransa. Akan hakan akan ne ministan tsaron Jamus, Thomas de Maiziere ya fada a cikin firar da gidan rediyon ya yi da shi cewa Faransa ita ce kadai kasar da ta shiga Mali domin murkushe kokarin da 'yan tawaye ke yi na kwace iko da kudancin kasar. Ministan ya kara da cewa ko da yake Jamus ba za ta shiga yakin da ake yi da 'yan tawayen ba, to amma za ta ba da taimakon kayan aiki. A yau Litinin ne komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai duba bukatar da Faransa ta mika game da halin da ke wakana a kasar ta Mali.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi