Sojojin Chadi uku sun mutu a kasar Kamaru | Labarai | DW | 31.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Chadi uku sun mutu a kasar Kamaru

Hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai yankin arewacin Kamaru ya yi sanadiyar rasa rayukansu dakarun kasar Chadi uku da kuma 'yan bindiga 123.

Gwamnatin Chadi ta tabbatar da mutuwar sojojinta uku a wasu hare-hare da kungiyar Boko Haram ta kai a arewain kamaru. Sai dai kuma cikin sanarwar da rudunar sojojin kasar ta bayar, ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe 'yan bindiga 123. Tun a ranakun Alhamis da kuma Jumma'a ne dai masu gagwarmaya da makamai suka kai hare-hare a kuri'ar arewacin kamaru, a daidai lokacin da sojojin kawance suka fara jan daga a garin Fotokol da ke da iyaka da tarayyar Najeriya.

Dakarun Chadi 1500 zuwa 2000 ne suke jibge a kasar kamaru yanzu haka don yakar kungiyar Boko haram da ta fara yada angizonta zuwa kasashen da ke makwabtaka da tarayyar Najeriya. Shugaba Idris Deby Itno ya riga ya bayyana aniyarsa ta karbo garin Baga da ya fada hannu 'yan Boko Haram tun farkon wannan wata na janairu bayan da suka kashe mutane da aka kiyasta cewa sun kai dubu biyu.

Kwamitin sulhu na AU ya bukaci kasashen mambobi su kafa rundunar sojoji da za ta kunshi mutane 7500 don ganin bayan kungyiar da ke fafutika da makamai a yankin Arewa maso gabashin tarayyar Najeriya. Hukumomin Abuja na hana ruwa guda a kokarin da Kasashen makwabtanta ke yi na kafa rundunar hadin guywa don kare iyakokinsu daga hare-haren yan bindiga na Boko Haram.